in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar ganuwa
2013-10-25 19:34:42 cri


SHIRIN ALLAH DAYA GARI BAMBAN

Danladi: Assalam Alaikum jama'a masu sauraro barka da har haka kuma barka da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin mu na ALLAH DAYA GARI BAMBAN daga nan sashen hausa na rediyon kasar Sin inda a yau ni Danladi zan ja akalar shirin tare da taimakon abokin aikina malamMaman Ada. Malam ADA barka da war haka yaya kuma aiki?

Maman: Assalamu alaikum jama'a, to Danladi lafiya kalau nike sannan kuma aiki da godiya tare da fatan haka ga masu sauraren sashen hausa na CRI. To Danladi me za mu tattaunawa a cikin shirin na yau a kai?

Danladi: Gaskiyarka Maman ADA, yau shirin ALLAH DAYA GARI BAMBAN zai maida hankali kan daya daga cikin muhimman abubuwan al'ajabi na tarihin kasar Sin wanda kuma yake alamanta kasar Sin a idon duniya. Ma'ana dai malam Maman ADA a yau za mu tattaunawa kan babbar ganuwa ta kasar Sin wato jigon shirin namu kenan da fatan kuma masu saurare zasu ara mana kunnuwansu.

Maman: Ai kam malam Danladi shirin na yau muhimmin shiri ne domin kam sau dama masu sauraren mu suke bayyana shawar irin wannan jigon shirin na ALLAH DAYA GARI BAMBAN, hakika babbar ganuwa wata babbar alamace ta kasar Sin a duniya kuma ina fatan masu saurare zasu biyo mu a cikin wannan shiri.

Danladi: To madalla malam Ada, kafin mu kutsa cikin gundarin shirin bari mu koma baya domin malam bahaushe nacewa waiwaye adon tafiya ta yadda za mu iyar kalato tarihin babbar ganuwa ta kasar Sin. Ita dai babbar ganuwa kamar yadda yawancin bayanan tarihi suka nuna, yawancin ginita ya fara ne a lokacin sarautar Ming daga bakin shekarar 1368 zuwa shekarar 1644. Kuma ta taso daga Jiayuguan na lardin Gansu a yammacin kasar Sin har zuwa bakin koginYalujiang na lardin Liaoning a arewa maso gabashin kasar Sin, sannan ta ratsa larduna da birane da kuma jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu guda tara bisa tsawon kilomita fiye da dubu bakwai. A halin yanzu babbar ganuwa ta kasar Sin ta kasance daya daga cikin abubuwan ban al'ajabi guda bakwai na duniya. A shekarar 1987 ne, kungiyar UNESCO ta sanya babbar ganuwa ta kasar Sin a cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi da aka gada na duniya.

Maman: Lalle malam Danladi bayaninka na nuna cewa babbar ganuwa tana kunshe da abubuwan tarihi dana al'ajabi da babban tasiri ga tunanin dan adam. Kamar yadda wasu bayanan tarihi suka nuna na cewa an fara gina ganuwa tun kafin karni na 9 wato kafin haifuwar Annabi Isa. Kuma a wancan lokaci amfani wannan ganuwa shi ne kare dauloli daga yaki da hare hare daga wajen abokan gaba.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China