Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso wanda yake halartar bikin tattauna batutuwan zuba jari da yin cinikayya na kasa da kasa karo na 17 da ake yi a kasar Sin, ya ce, kara turo matasa da malamai na jihar Kano da su zo kasar Sin su koyi harshen Sinanci, hakan zai sa karin 'yan Najeriya su san al'adun Sinawa da harshen Sinanci, har ma jihar Kano za ta iya hawan jirgin kasan da kasar Sin ke tukawa wajen bunkasa tattalin arziki.
Bugu da kari Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, wannan taron tattauna batutuwan zuba jari da yin cinikayya na kasa da kasa ya kasance tamkar wani muhimmin dandali ga wakilan kasashe daban daban wajen tattauna halin da tattalin arziki ke ciki a duniya, batun kara zuba jari da yin cinikayya tsakanin kasa da kasa. Ya kara da cewa, a yayin bikin, gwamnatin jihar Kano ta yi musayar ra'ayoyi da masu zuba jari na kasar Sin kan yadda za su iya zuba jari a jihar a fannonin gine-gine, aikin gona, hakar ma'adinai da shimfida hanyoyin mota. Yana fatan bangarorin biyu za su iya hanzarta tafiyar da yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa da suka kulla. (Sanusi Chen)