A nasa bangaren kuma, ministan babban birnin tarayya Senata Bala Mohammed ya bayyana yadda wannan aikin shimfida layin dogo a Abuja yake. Ga abun da yake cewa:
"Wannan jirgin kasa, wanda gwamnatin tarayya take yi kuma take taimakon birnin tarayya na Abuja tayi, da kudade masu dimbin yawa sama da dala miliyan 863, wanda tuni gwamnatin kasar Sin ta ba mu bashin miliyan 500, mu kuma mun kara bada sauran. Yanzu wannan shi ne na farko da muka zo, amma sauran duk za'a bi a gina su, ciki akwai wajen hutawa, akwai wajen cin abinci, akwai wajen nishadi, akwai wajen otel, da sauransu. Ina kira ga al'ummar Najeriya su ci gaba da ba mu goyon-baya, da kuma taimakawa wajen fahimtar da al'umma, cewa abubuwan da gwamnati take yi, ba na gwamnati ba ne, nasu ne."