130724murtala
|
Ministan babban birnin tarayya wato FCT Senata Bala Mohammed, da babban manajan kamfanin CCECC reshen Najeriya Mista Shi Hongbing, da sarakunan gargajiya dake birnin Abuja, tare kuma da sauran wasu jami'an gwamnati ne suka halarci wannan buki.
A cikin jawabin da ya gabatar, Mista Shi Hongbing na kamfanin CCECC ya ce, bikin da aka yi yau, wato bikin kaddamar da aikin gina tashar National Park ta layin dogo na Abuja, ya nuna cewa an samu babban ci gaba ta fannin shimfida layin dogo a birnin Abuja, kuma kamfanin CCECC zai ci gaba da yin hayar ma'aikata 'yan Najeriya a wajen wannan aiki. Ga abun da yake cewa:
"Za mu ci gaba da yin hayar ma'aikata 'yan Najeriya, da horas da karin mazauna gurin ta fannin fasaha. Kawo yanzu, akwai ma'aikatan kasar Sin kimanin 80 a wannan aiki, amma adadin yawan ma'aikatan Najeriya a nan ya zarce dubu 2. Haka kuma bayan da muka kammala aikin, za mu yi hayar ma'aikata 'yan Najeriya sama da dubu 3. Har wa yau kuma, mun kafa wata makarantar samar da horo a Idu, inda a yanzu haka muke horas da ma'aikata 'yan Najeriya dari 1 kowace rana."