Ministan tsaron kasar Gabon, Pacome Rufin Ondzounga da takwaransa na cikin gida, Jean Francois Ndongou, sun kai wani rangadin aiki a birnin Port-Gentil yankin hakar man fetur kuma cibiyar tattalin arzikin kasar Gabon, domin sanar da maida martanin da aka shirya kan murkushe 'yan fashin teku da suka dauki yin daga da kasar bayan da suka yi garkuwa da wani jirgin ruwan jigilar man fetur da ya zo daukar dayen man fetur a tashar ruwan Cap Lopez, a wani labarin da aka samu a ranar Lahadi daga ma'aikatar tsaron kasar Gabon.
A ranar 15 ga watan Julin da ya gabata ne, 'yan fashin teku da ake zaton 'yan asalin kasar Najeriya sun yi garkuwa da jirgin ruwan Tanker Cotton mai lambar IMO 9380380 tare da mambobin jirgin ruwan 24 'yan asalin kasar Indiya a yayin da jirgin zuwansu ya zo daukar gurbataccen man fetur a tashar ruwan Cap Lopez. (Maman Ada)