Tsinken da Sinawa ke amfani yana tafiya da zamani. Muna iya gano tsinkaye iri iri sama da 100 a tarihin kasar Sin, amma a takaice, muna iya karkasa su cikin gida biyar, wato irin da aka yi da itace, irin da aka yi da karafa, irin da aka yi da hakora ko kasussukan dabbobi, irin da aka yi da dutse da kuma irin da aka yi da kaya na zamani, misali roba. A farkon fari, an yi amfani da icen da aka tsinta daga itace ko kuma hakora da kasussukan dabbobi wajen yin tsinke, amma bisa ci gaban zaman al'umma, an kuma fitar da tsinken da aka yi da karafa ko wani nau'in dutse mai daraja da ake kira Jade. Muna iya tunawa da zamanin gargajiya ta Tang, lokacin da aka fitar da tsinken da aka yi da zinari da kuma azurfa. Amma a lokacin, sai masu sarauta ne kawai ke iya amfani da tsinken da aka yi na zinari, kuma tsinken da aka yi da azurfa na samun karbuwa sosai a wurin masu hannu da shuni. A zamanin yanzu, muna kuma da tsinken da aka yi da kaya na zamani, misali roba, duk da haka, tsinken da ya fi samun karbuwa irin da aka yi da ice ko icen gora.
Har wa yau, akwai al'adun Sinawa da ke shafar tsinke. Misali a wasu sassan kasar Sin, lokacin da ake bikin aure ko sauran bukukuwa, a kan nuna wata rawar da aka yi da tsinke. Bayan haka, sabo da kullum da tsinke biyu ne a kan ci abinci, shi ya sa tsinke ya zama wata alamar alheri ga ma'aurata a wasu sassa, musamman a wajen bikin aure, a kan ba ango da amarya kyautar tsinkaye biyu, domin yi musu fatan alheri na rike amana da juna har abada. Bayan haka, akwai wasu abubuwa da aka haramta game da tsinke da al'adar Sinawa, misali, lokacin da ake cin abinci, bai kamata a buga kwano da tsinke ba, sabo da ana ganin sai fakirai ne ke yin wannan lokacin da suke bara.