130718-dan-wasan-tseren-kasar-Habasha-Gebrselassie-ya-nuna-shaawar-shiga-dandalin-siyasa-zainab
|
Wani babban abin da ya sa Sinawa su bambanta da al'ummomin sauran sassan duniya ita ce al'adarsu ta cin abinci, wato yadda suke cin abinci da tsinke, kamar yadda al'adar cin abinci da cokali take ga kasashen Turawa, cin abinci da hannu ga mutanen Afrika to haka al'adar cin abinci da tsinke take ga Sinawa, kuma ita wannan al'ada tana daga cikin al'adun Sinawa mafi jimawa a duk fadin kasar, ka hana Basine cin abinci da tsinke to tamkar ka rage masa wani sashen zaman rayuwa ne mai muhimmanci.
Wannan al'ada ta cin abinci da tsinke a kasar Sin, muna iya cewa ta fara tun shekaru aru aru kimanin dubu hudu da suka wuce. Bisa ga nazarin da aka yi, a lokacin, kaka da kakanin Sinawa wadanda ke zama cikin dazuzzuka, su kan tsinci itace domin yin amfani da shi wajen dafa abinci da cin abinci, domin ka ga abinci na da zafi sosai lokacin da ake dafa shi, shi ya sa ba sai a yi amfani da hannu kai tsaye ba, dole a samu wani kaya, to, haka irin itacen ya zama asalin tsinken da ake amfani da shi a halin yanzu.