in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ecuador ta tabbatar da samun mafakar siyasa daga Snowden
2013-06-24 12:26:25 cri

Mahukuntan kasar Ecuador sun bayyana cewa, sun samu bukatar neman mafakar siyasa daga tsohon 'dan kwangilar hukumar tsaron farin kaya ta Amurka NSA mai suna Edward Snowden, mutumin da kasar Amurkan ke zargi da tona asirin wasu sirrikan tsaron kasar, da suka jibanci shirin leken asiri da gwamnatin ke gudanarwa ta yanar gizo, da kuma layukan wayoyin jama'a.

Ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Ecuador Ricardo Patino ne ya bayyana hakan a kasar Vietnam, yayin wata ziyarar aiki da yake gudanarwa, yana mai cewa,sun samu sakon Snowden ne ta shafinsa na Twitter. Ko da yake, Patino bai tabbatar da ko kasar tasa za ta amince da bukatar ta Snowden a yanzu haka ba, a baya ya taba cewa, akwai yiwuwar Ecuador ta duba wannan bukata, muddin dai wancan 'dan kwangila ya nuna sha'awar samun mafaka a kasar.

A wani ci gaban kuma wasu rahotanni daga kafofin watsa labarun kasar Rasha, sun bayyana cewa, Snowden ya sauka a Moscow ranar Lahadi 23 ga wata, bayan ya baro yankin musamman Hong Kong na kasar Sin ya kuma samu tarya daga jakadan kasar Ecuador dake birnin na Moscow.

Tuni dai kungiyar tonon asirin nan da ake kira da "WikiLeaks", wadda Julian Assange ya kafa, ta ce, Snowden zai shiga kasar Ecuador domin samun mahafa, kuma lauyoyinta za su dauki matakan kare masa 'yancinsa a matsayinsa na bil'adama. Shi ma dai jagoran na WikiLeaks Julian Assange, yanzu haka na can ofishin jakadancin kasar Ecuador dake Birtaniya, inda yake samun mafaka. A kokarinsa na kaucewa maidashi kasar Sweden da jami'an tsaro ke son yi, tare da gurfanar da shi gaban kotu, bisa wani zargi na aikata laifuka masu alaka da cin zarafin mata da ake zarginsa da aikatawa a kasar ta Sweden. Ko da yake Assange ya samu damar samun mafakar siyasa a kasar ta Equador, rashin kariya daga Birtaniya ta sanya shi kasa fita daga ofishin jakadancin kasar ta Ecuador dake can. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China