in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnan Kano a tarayyar Nijeriya ya jagoranci kona jabun magunguna na sama da naira miliyan 900
2013-06-17 16:28:15 cri

Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya cigaba da cewa, da yawa daga cikin mutane da suke sayen irin wadannan magunguna, ba sa samun waraka daga irin cututtukan dake damunsu . Wasunsu ma su na rasa rayukansu bayan sun yi amfani da magungunan sabo da rashin ingancinsu.

Haka kuma gwamnan ya kara da cewa, sayar da irin wadannan magunguna na jabu sun kara cusa matasa cikin harkar shan miyagun kwayoyi dake gusar da tunani.

Injinya Rabi`u Musa Kwankwaso ya jaddada kudirin gwamnatinsa na amfani da dokokin da suka kamata wajen yakar sana`ar sayar da miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen bikin kone jabun magungunan, daraktan lura da miyagun kwayoyi na hukumar tabbatar da ingancin magunguna da abinci ta Najeriya NAFDAC Pharmacy Ubale Hashim ya ce a halin yanzu `yan sandan kasa da kasa suna aikin sirri domin kame nau`in magungunan da ake shigowa da su Najeriya daga kasashen Turai.

Daga cikin jami `an da suka ganewa idanunsu yadda aka kone magungunan, sun hada da kwamashinan `yan sandan jihar Kano Alhaji Muhammad Daura da shugaban hukumar kare hakkin masu sayen kaya ta kasa shiyyar Kano Alhaji Nuhu Bello da kuma kwamandan shiyyar jihar kano na hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA.(GARBA ABDULLAHI BAGWAI)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China