A ranar Laraba ce, kwamitin tsaro na MDD ya kara wa'adin aikin cibiyar majalisar domin karfafa da tabbatar da zaman lafiya (BINUGBIS) dake kasar Guinee-Bissau har zuwa ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2014.
Kudurin mai lamba 2103, ya wuce da babban rinjaye, sannan kuma kudurin ya bukaci dukkan dakaru masu makamai da su komawa a karkashin gwamnatin kasar ba tare da wani sharadi ba. Hakazalika, kwamitin tsaro ya jaddada muhimmancin fatansa na ganin an shirya zabubuka cikin 'yanci da adalci domin tabbatar da sake maido da doka da oda a kasar nan da karshen shekarar 2013, tare da yin kira ga babban sakataren MDD da ya ba da taimakon shirya zabe ta hanyar babban manzonsa na musammun kan kasar Guinee-Bissau da BINUGBIS, mista Jose Ramos Horta.
A ranar 9 ga watan Mayun da ya gabata, mista Ramos ya yi jawabi gaban kwamitin tsaro, inda ya bukaci da a kawo gyaran fuska kan wa'adin tawagar siyasa ta MDD dake kasar Guinee-Bissau, wadda a shekarar da ta gabata ta yi fama da juyin mulki.
A karshe kuma, wannan kuduri na MDD ya nuna damuwarsa kan tsanantaccen fasa kwaurin kwayoyi a cikin kasar ta Guinee-Bissau tun bayan juyin mulkin sojojin kasar, tare da yin kira ga hukumomin kasar da su dauki nagartattun matakai da dokoki domin daidaita wannan annnoba da matsalar halaltar da kudin haram. (Maman Ada)