in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shigowar kasar Sin a kungiyar WTO na kawo moriya ga bangarori daban daban
2011-12-06 15:22:43 cri

A lokacin da aka cika shekaru 10 da shigar da kasar Sin cikin kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), babban jami'in kungiyar WTO Pascal Lamy ya shedawa manema labaru cewa, shigowar kasar Sin a kungiyar WTO na kawo babbar moriya ga bangarori daban daban.

Mr. Lamy ya ce, bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, kamfannonin kasar Sin sun samu karin damar yin cinikayya a duniya, kuma sun samu tabbaci sosai a fannin kiyaye moriyarsu. A sa'i daya, hakan ya samar da karin dama ga kamfannonin kasashen waje wajen yin ciniki a kasar Sin, kuma ya ba su kwarin gwiwa wajen shiga kasuwar kasar Sin. Ban da haka kuma, shigowar kasar Sin a kungiyar WTO ya kawo moriya ga kamfannonin kasar Amurka da kasashen Turai da kuma sauran kasashen kungiyar WTO.

Bugu da kari, Mr. Lamy ya bayyana cewa, kasar Sin ta sauke nauyin da kungiyar WTO ta dora mata yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China