in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Cote D'ivoire ta yi tir da harin da aka kai bayan zaben kananan hukumomi
2013-04-25 16:36:19 cri

A gun taron manema labarai da kakakin gwamnatin kasar Cote D'ivoire Bamba Lamine ya kira a ran 24 ga wata a birnin Abidjan babban birnin kasar, ya yi tir da tashe tashen hankalin da aka tayar a wurare daban-daban na kasar bayan zaben kananan hukumomin birane da garuruwan kasar.

Mr Bamba Lamine da ya yi Allah wadai da ko wane hari, yana mai cewa, ba a yarda da yin amfani da karfin tuwo ba ko kusa. Daga nan sai ya yi kira ga 'yan takara da magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu a yayin samun sakamakon zaben, su kuma fararen hula su mutunta sakamakon da kwamitin zaben mai zaman kanta za ta gabatar.

A ran 21 ga wata ne kasar ta Cote D'ivoire ta gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar. Tun lokacin da kwamitin zaben ya fara bayyana sakamakon zabe daga ran 22 ga wata, aka rika samun rikice-rikice, abin da ya jawo raunuka ga matane da dama. Masu goyon baya 'yan takara sun taru suka yi zanga-zanga domin nuna takaici kan magudi da aka tabka a zaben. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China