in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban kasar Sin zai kai ziyara a Rasha da Afirka, in ji ministan harkokin wajen kasar
2013-03-09 16:39:19 cri
Sabon shugaban kasar Sin zai kai ziyarar farko a kasashen Rasha, Tanzania, Afirka ta kudu da kuma Jamhuriyar Congo, kana zai halarci taron shugabanin kasshen kungiyar BRICS jiko na biyar a Durban, in ji ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi.

Za'a yi taron na BRICS ne daga 26 zuwa 27 ga watan Maris a Durban na kasar Afirka ta kudu.

Da yake magana kan wannan ziyarar da shuagaban zai kai Rasha. Yang ya ce kasar Sin na fatan amfani da wannan dama wajen kara sa kaimi kan dangataka dake tsakanin Sin da Rasha.

Yang ya yi magana ne yayin taron manema labarai a gun taron majalisar kasar Sin na shekara-shekara inda ya ce Rasha da kasar Sin manyan makwabta ne ga juna kuma suna daukar kansu a matsayin muhimman abokan tafiya a fuskar ci gaba da kuma hada gwiwa.

A yayin wannan babban taro na jama'ar kasa ne za'a bullo da sabbin shugabannin kasar Sin kuma za'a kare taron ran 17 ga watan Maris.

Yang ya ce ziyara da sabon shugaban zai kai Afirka babbar alama ce ga irin kaimi da kasar Sin ke dorawa kan dangantakarta da kasashen Afirka.

Ministan na mai fatan wannan ziyara ta sabon shugaban za ta inganta kawance tsakanin kasashen BRICS, kawo habbaka ga burin kungiyar da kuma kara kyautata kawance tsakanin kasashen kungiyar BRICS da kasashe dake nahiyar Afirka da ma sauran yankuna.

Ya ci gaba da cewa BRICS ta zamo muhimmiyar kafar kariya na matsalar hada hadar kudi a duniya ta hanyar kawo bunkasar tattalin arziki, kara kyautata tattalin arzikin duniya da kuma inganta dumokradiya a kawancen kasa da kasa.

Kungiyar BRICS kungiya ce ta bunkasa tattalin arziki dake wakiltar kasashen masu tasowa a fannin tattalin arziki wato Brazil, Rasha, India, Sin, da kuma Afirka ta kudu.

Kasashe mambobin kungiyar BRICs suna da yawan jama'a da suka kai kashi 43 cikin dari na yawan mutanen duniya kuma su ne suke da a kalla kashi daya cikin biyar na GDP a duniya wato yawan albarka da ake samu daga sarrafa albarkatun kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China