in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Drogba: Mafarki na game da lashe gasar AFCON ya kare
2013-02-07 20:19:36 cri

Shahararren dan wasan nan, kuma kefdin din kasar Ivory Coast Didier Drogba, ya bayyanawa manema labaru cewa, mafarkin sa, na jagorantar kungiyar kasar sa, domin lashe kofin nahiyar Afirka ya kare, duba da cewa watakila wannan ce shekarar karshe da zai halarci wannan gasa tare da ragowar 'yan kungiyar ta Ivory Coast.

Drogba dan shekaru 34 da haihuwa, wanda ya bayyana hakan bayan Kulaf din Super Eagles na Nigeria ya lallasa su da ci 2 da 1 ranar Lahadin data gabata, a wasan da suka yi na daf da na kusa da na karshe, ya kara da cewa lokaci yayi da zai dau hakuri kan wannan rashin nasara da ta same su, dama kudirin daukar kofin ga kasar sa.

Ta-leko-ta-koma da wannan kofi na AFCON ya dade yana yiwa Ivory Coast nada dogon tarihi, domin kuwa duk da irin manyan 'yan wasan da kasar ke da su, sau daya tak suka taba daukar sa, wato a shekarar 1992, sai dai na biyu da suka zo sau 2. Wani abun ta'ajibi ma shi ne yadda sau 8 a jere ana zatorwa Ivory Coast din daukar wannan kofi amma hakan taci-tura.

Yayin fitar su daga filin wasa bayan kammala wasan na ran Lahadi , 'yan wasan Ivory Coast din da aka san su da rera wakokin nuna farin ciki, a wannan karo sun fita salin-alam ba tare da yiwa kowa magana ba.

Sai dai a nasa bangare kocin kungiyar Sabri Lamouchi kare 'yan wasan nasa ya yi, yana mai cewa sunyi rawar gani, koda yake sun samu damar shigewa gaba, amma suka gaza amfani da ita yadda ya dace. Lamouchi wanda ya karbi aikin horas da 'yan wasan wata guda kacal kafin fara gasar ta AFCON ta bana, yana fatan nan gaba zasu sake farfadowa, su kuma yi abinda ya dace da matsayin su.

Shima wani dan wasan Ivory Coast din Bamba cewa yayi, rashin nasara hanya ce ta gane kurakurai, yana fatan zasu yi amfani da

basirar su wajen taka rawar gani a wasan cin kofin duniya dake tafe a shekara mai zuwa, kamar dai yadda shi ma Drogba ya bayyana yayin tattaunawar sa da 'yan jaridu. (Samunu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Gasar AFCON ta Shekarar 2013 2013-01-08 12:17:15
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China