Sai dai a wannan lokaci wata gaba ce ta bakin ciki gare su, duba da yadda suka shirya kayan su domin adabo da wannan gasa, dake wakana a Afirka ta kudu, bayan da Burkina Faso ta cire su a yayin wasan su daya gabata. Duk da hakan manazarta harkokin wasanni na ganin ba za a kwatanta yanayin a wannan karo da abin da ya same su a wancan lokaci ba. Musamman idan aka kalli irin wasannin da suka samu nasarar su kafin a fidda su.
Hakan ne ma ya sanya Kocin kungiyar Didier Six, bayyanawa manema labaru gamsuwar sa, don gane da irin rawar da 'yan wasan nasa suka taka. Six yace sunyi takaicin cire su da aka yi a wannan matsayi na gasar, amma ya tabbata sun samu nasara zuwa wannan gaba, kuma akwai hasken nasara ga kulaf din nan gaba, duba da irin matasan 'yan wasa da ke tasowa a cikin sa.
Shima mataimakin keftin din kulaf din Serge Akakpo cewa yayi har kwanan gobe, suna jin radadin waccan ta'asa da akai musu a Cabinda, yana mai cewa bayan aukuwar wannan lamari "naji kamar na fasa ci gaba da bugawa kulaf din kasar tamu wasa, amma daga bisani naga dacewar cigaba da wasa ga kasar tawa, a yanzu muna buga dukkanin wasannin mu, tare da sadaukar da nasarar ga wadancan 'yan wasa namu da suka rasu, sakamakon harin na Cabinda, muna musu addu'a da fatan samun rahama" . A kalaman Akekpo.
Togo dai ta samu zuwa gasar AFCON ta bana ne bayan da a bara suka gaza fitowa daga zagayen fidda gwani na kasashen yankin su, kuma abin mamaki sai gashi a bana sun fito da karfi, sun kuma yi bazata, musamman ganin yadda suka ketare shingen rukunin su na 4, da ya hada kasashe masu zafi kamar Ivory Coast, da Tunisia, da Algeria, suka kuma samu nasarar zama na biyu a rukunin.(Saminu Alhassan Usman)