'Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun nuna matsayinsu na tsaffin hannu a gasar cin kofin nahiyar Afirka a jiya Laraba, bayan da suka lallasa kasar Mali da ci 4 da 1, yayin wasan da aka buga a filin wasa na Moses Mabhida.
Wannan wasa wanda ya kayatar matuka, kusan a iya cewa, an kammala muhimmin bangarensa ne tun a farkon rabin lokaci, inda cikin minti na 25 Elderson Echiejile ya jefa wa Najeriya kwallon farko, sai kwallo ta biyu a minti na 30, ta hannun Brown Ideye, kafin daga bisani dan wasan Mali Momo Sissoko ya jefa kwallo ta 3 a ragar kasarsa, yayin da yake kokarin fidda kwallon da Emenike ya bugo.
Kwallon Najeriya na karshe, ta hannun Ahmed Musa, ta shiga zaren Mali ne a minti na 56, ko da yake dai su ma sun jefa kwallon ladan ganin ido a mintuna 15 kafin tashi daga wasan ta hannun Chieck Diarra.
Haka dai aka tashi wannan wasa Najeriya na da ci 4, Mali nada kwallo 1, wanda hakan ya sanya Super Eagles su shiga wasan karshe a ranar Lahadi mai zuwa, domin fafatawa da kasar Burikina Faso, karon farko da ita Burkina Fason ta kawo ga wannan matsayi. Yayin da ita kuwa Najeriya ke burin daukar kofin a karo na 3 a wannan lokaci.
Sai kuma wasan Burkina Faso da Ghana da ya gabata, da ya kasance muhimmin wasa a tarihin kofin AFCON, ganin yadda daga karshe Ghana ta fice daga gasar ta hannun kasar da ba a za ci za ta iya cire ta ba. Ko da yake dai Burkina Fason na da 'yan baya masu ban mamaki, wadanda tun farkon gasar aka bayyana cewa, suna cikin mafiya nagarta cikin dukkanin kasashen da suka zo gasar ta bana.
An dai kai ruwa rana a filin wasa na Nelspruit, inda Ghana dake burin kaiwa ga daukar kofin na bana a karo na 5 ta fice ba zato, bayan da wasan ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Kafin hakan dai dan wasan Ghana Mubarak Wakaso ne ya ci wa kasar tasa kwallo, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, kafin daga bisani a minti na 60 Aristides Bance ya farke wa Burkina Faso wannan kwallo. Baya ga wannan kwallo Bance ya yi ta kai hare-hare, wadanda wasun su golan Ghana Fatau Dauda ya kawar, yayin da su ma masu tsaron gida suka yi nasu kokari na hana kwallayen shiga ragarsu.
Dan wasan Ghana Isaac Vorsah ne dai ya fara zubarwa kasar sa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan an kammala karin lokaci da aka sanyawa karshen wasan, lokacin da kwallo da ya buga ta baude. Haka aka ci gaba da bugun daga kai sai gola, har zuwa lokacin da Bance ya buga kwallon karshe da ta sanya Burkina Faso shigewa gaba da Kwallaye 3, yayin da kuma Ghana ta yi baya, bayan da Emmanuel Agyemang Badu ya zubar da tasa kwallo. Wato dai an tashi wasan Burkina Faso na da ci 3 Ghana nada kwallaye 2 ke nan.
Yanzu dai a iya cewa, wasan da ke gaba shi ne na neman kasar da za ta zamo ta 3, wanda za a buga tsakanin Ghana da Mali a ranar Asabar 9 ga wata. Sannan kuma a kece reni tsakanin Najeriya da Burkina Faso a washe gari, wato ranar Lahadi 10 ga wata. A wasan da zai baiwa Burkina Faso damar daukar wannan kofi a karo na farko, tun yunkurin ta na karshe a shekarar 1998, lokacin da aka fidda su a farkon zagayen gasar na biyu da aka yi a kasar su. Ko kuma Nigeria da ke kwalamar wannan kofi shekaru 19 ke nan da daukar sa na karshe, wato a shekarar 1994.(Saminu&Ibrahim)