A ranar 6 ga watan Disamba na shekarar 2007, bisa iznin da sashen koyon Sinanci na kasar Sin ya bayar, gidan rediyon CRI ya kafa kwalejin Confucius na koyon Sinanci ta hanyar rediyo, wanda ya bude sabon shafi na yada Sinanci a fadin duniya ta CRI.
A shekaru biyar da suka gabata, kwalejin ya yi amfani da harsuna mafiya fifiko da dama da fasahohin rediyo, da bin tunanin "yin amfani da harshen wurin wajen koyar da Sinanci", da kafa kwalejojin koyon Sinanci 12 a kasashen Kenya, Bangladesh, Pakistan, Italiya da sauran kasashen duniya, kana an gabatar da litattafan karatu ta harsuna da dama, da gina dandalin koyon Sinanci ta hanyar rediyo, internet, IPTV da dai sauransu, da kuma gudanar da aikin yada al'adu kamar "Sannu, kasar Sin". (Zainab)