Ya kara da cewa, yana da dimbin aikin da ke gabanshi, kuma ya yi alkawarin yin batau ga kasarsa .
Ya kara da cewa, "na ji dadi da na kasance wanda ya kawo abun da ake tsammani, wannan rana ta 6 ga watan Mayu za ta kasance wata babbar rana ga kasarmu, wani sabon tubali ga nahiyar Turai, sabon tsammamni ga duniya".
Ya nuna da cewa, zai kasance shugaba na kowa da kowa, inda ya ci gaba da cewa, "a wannan yammaci babu kasar Faransa biyu, kasa daya ce, a cikin hadin kai a wuri guda. Kowa zai kasance daidai da kowa ta fannin doka da aiki. Tangarda da dama, tsaiko da dama, sun rarraba kanun 'yan kasarmu, wannan ya kare! A yau ina tambaya da a auna ni ta yin la'akari da abubuwa guda 2, shari' a da matasa, a cewar Francois Hollande.(Abdou Halilou).