in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta shiga sabon lokacin samar da gidajen inganta rayuwar jama'a
2011-03-10 17:23:35 cri

Haka kuma, Mr. Qi Ji, mataimakin ministan kula da harkokin gidajen kwana da bunkasa birane da yankunan karkara na kasar Sin ya bayyana cewa, "Game da kudin gina gidajen inganta rayuwar jama'a, dole ne a sanya shi cikin kasafin kudin gwamnatin wurare daban daban. Yanzu muna nazarin manufofin yadda hukumomin kudi za su tallafawa wannan aiki, musamman yadda za su ba da rancen kudi na matsakaci da dogon lokaci ga wadanda suke da nasaba da samar da gidajen inganta rayuwar jama'a. Bugu da kari, muna tsara manufofin jawo hankalin kamfanoni da su shiga aikin gina gidaje masu rahusa."

Birnin Chongqing ya yi kokari sosai wajen samar da gidaje masu rahusa ga mutane masu karamin karfi a cikin 'yan shekarun nan. Yayin da yake ganawa da wakilan kafofin watsa labaru a nan birnin Beijing, Mr. Huang Qifan, magajin birnin Chongqing ya bayyana musu shirin da ake na samar da gidajen inganta rayuwar jama'a, cewar, "A bara, yawan gidajen inganta rayuwar jama'a da muka soma ginawa ya kai murabba'in mita miliyan 13, sannan muna da shirin samar da gidaje masu rahusa da yawansu ya kai murabba'in mita miliyan 40 a cikin shekaru 3 masu zuwa. Idan wani mazauni ya iya samun murabba'in mita 20, to, wadannan gidaje za su iya biyan bukatun da mazauna miliyan 2." (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China