in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta shiga sabon lokacin samar da gidajen inganta rayuwar jama'a
2011-03-10 17:23:35 cri

Aikin samar da gidaje masu rahusa yana jawo hankalin mutane masu karamin karfi. Tabbatar da ganin kowa ya samu wurin kwana muhimmin nauyi ne da aka dora wa gwamnatin kasar Sin bisa rahoton da firaminista Wen Jiabao na kasar ya gabatar. Bisa shirin da gwamnatin kasar ta yi, za a samar da gidaje masu rahusa miliyan 10 a bana ga mutane masu karamin karfi. Sannan za a gyara gidaje masu fuskantar hadari miliyan 1 da dubu dari 5 a yankunan karkara. Game da wannan shiri, Mr. Wang Dacheng, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Mutane da yawa ba su son kashe kudi kan ayyukan samar da gidajen ingantan rayuwar jama'a. Sabo da haka, ya kamata gwamnati ta canja irin wannan halin da ake ciki, kuma ta tsara shirin samar da gidajen inganta rayuwar jama'a lokacin da take tsara shirin sarrafa dukiyar kasa."

Sannan, Mr. Yang Kaisheng, wani mamba daban na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya ce, "Ya kamata bankuna da gwamnatoci a matakan wurare daban daban da wasu kamfanonin samar da gidajen kwana su yi nazari tare kan yadda za a samar da kudin gina gidajen inganta rayuwar jama'a."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China