A sakamakon haka, abin da ya faru a wannan karo tsakanin jiragen ruwan kamun kifaye na Sin da Japan, abu mafi muhimmanci shi ne, lamarin ya abku ne a wurin da kasashen biyu suka dade kowanne a cikinsu ke ikirarin mallaka. A sabili da haka, a matsayinta na kasar da ta haddasa wannan lamari, Japan ba ta nemi gafara ko kadan. Hakan ya tilasta kasar Sin da ta dauki matakai nan take. A karshe Japan ta saki kyaptin din na kasar Sin. Duk da haka, lamarin ya yi babbar illa ga dangantaka tsakanin Sin da Japan har zuwa yanzu.
Tsibiran Diaoyu suna kasancewa a iyakar gabas da tekun kasar Sin, kuma fadinsu ya kai murabba'in kilomita 6.5. Mutanen Sin ne suka fara tarar da su, kuma suka rada musu suna. Ko da yake babu mutanen dake zaune a wurin, amma an tabbatar da cewa, kasar Sin ta mallaka wadannan tsibirai tun daga shekaru 600 da suka gabata. Bayanan tarihi da yawa sun yi nuni da cewa, ko shakka babu kasar Sin tana da ikon mallakar tsibiran Diaoyu. Farfesa Yang Bojiang dake aiki a kwalejin dangantakar kasashen duniya na Sin ya jaddada cewa,
"Kamar yadda tarihi ya nuna ko bisa dokokin kasashen duniya, ko shakka babu kasar Sin tana da ikon mallakar tsibiran Diaoyu."
To, a sakamakon haka, ina dalilin da ya sa ake samu tashin hankali kan ikon mallakar tsibiran Diaoyu tsakanin Sin da Japan? A hakika dai, wannan matsala ta samo asali ne a karshen karnin 19 da ya gabata. A daidai wannan lokaci, kasar Japan tana kai hare-hare ga sauran kasashen duniya a kokarin kara yankunan mulkin kasar.
A lokacin, karfin kasar Sin ya ragu sosai. Sa'an nan sai Japan ta tsara taswirar kasarta, inda ta hade da tsibiran Diaoyu. Kuma ta ba su suna Senkaku. Daga bisani, bayan yakin duniya na biyu, bisa sanarwar Cairo da ta Potsdam, kamata ya yi Japan ta danka wadannan tsibiran ga kasar Sin. Amma Japan ba ta cika alkawarinta ba. Wannan ya sa gwamnatin kasar Sin ta nuna rashin amincewarta a kullum.
Abin tambaya shi ne yaya magance matsalar dangantaka tsakanin Sin da Japan da lamarin ya haddasa cikin gajeren lokaci? Wani masani kan harkokin Japan dake hukumar nazari kan harkokin duniya ta jami'ar mai suna Tsinghua Liu Jiangyong ya furta cewa, kamata ya yi kasashen biyu su yi kokari tare da zummar daidaita wannan matsala yadda ya kamata. Liu ya ce,
"Kasashen Sin da Japan suna kasancewa kan matsayi na daban. Shi ya sa suke fuskantar matsala kan yadda za su daidaita wannan matsala yadda ya kamata. Gwamnatocin kasashen biyu sun tabbatar da cewa, za a kara kiyaye da bunkasa dangantakar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. A sakamakon haka, an samu babban tushen daidaita wannan matsala."
To, jama'a masu karanta, bayani ke nan kan tambayar malam Ahmed, da fatan kana gamsu da dan takaitaccen bayanin da muka samar maka game da bayanin da ka nemi kan tsibiran Diaoyu mallakin kasar Sin.(fatima)