Haka ne, malam Sule Abdu Indabawa da malam Ibrahim Tijjani A. Gyaranya a Nijeriya. Kwamitin ba da lambar yabo ta Nobel yana gudanar da ayyukansa bisa ra'ayoyin kasashen yammacin duniya ke nan. Yana nuna hammaya ga kasar Sin a maimakon amincewa da kuma taimaka mata wajen kara samun ci gaba. Ma iya ce lambar yabon zaman lafiya ta Nobel ta riga ta zama wata na'ura dake hannun kasashen yammacin duniya a fannin siyasa. Muna fatan, lambar yabo ta Nobel za ta kama daidaitacciyar hanya ba tare da bata lokaci ba.
Bayan haka, malam Bello Gero a Sokoto, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Ina mai amfani da wannan dama ne domin in bayyana nawa ra'ayi a kan cika shekaru goma da kafa dandali hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyarmu ta Afirka. Ba shakka an samu gagarumin ci gaba tsakanin nahiyar Afirka da kasar Sin ta fannoni daban daban kamar tattalin arziki, sha'anin noma da raya kasa, kanfanoni, al'adu da kuma ba da tallafi, sha'anin sadarwa da dai makamantansu. An sami ci gaba matuka tun daga lokacin da kasar Sin ta soma wannan dandalin hadin gwiwa, kasashenmu na Afirka suka soma farfadowa ta fannoni daban daban a cikin wadannan shekaru goma. Bayan shigowar kasar Sin a nahiyar Afirka, mutane da yawa sun sami ci gaban arzikinsu ta fannoni da dama. Da karshe ina fatan Allah shi taimake mu ba kidaya amin."
To, mun gode, malam Bello Gero. Mu ma muna farin ciki sosai domin cika shekaru 10 da kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Da fatan za mu kara samun ci gaba tare a fannonin tattalin arziki, cinikayya, al'adu, fasahohi da dai sauransu. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.
Sakon malam Bello Gero ke nan. A kwanan baya, malam Ahmed Abbas a Kano, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Na ji an ce, a kwanan baya, an yi hadarin jiragen ruwa tsakanin Sin da Japan a tekun dake kusa da tsibiran Diaoyu. Don Allah ko za ku iya mana karin bayani kan lamarin?" To, malam Ahmed Abbas, bari mu kokarta amsa wannan tambaya, da fatan kana sauraronmu.
A watan Satumba na bana, a yankin tekun dake kusa da tsibiran Diaoyu na Sin, jiragen ruwan sintiri na hukumar kiyaye tsaron tekun kasar Japan guda biyu sun yi karo da wani jirgin ruwan kamun kifaye na kasar Sin. Daga bisani, sai Japan ta cafke kyaptin din jirgin ruwa na kasar Sin Zhan Qixiong. Hakan ya girgiza mutanen Sin da suke rayuwa a tsibiran Diaoyu da tsibiran dake kewayensu kwarai da gaske. Kuma al'amarin ya bata musu rai sosai da sosai. Kasar Sin ce kula da ikon mulkin tsibiran Diaoyu sama da shekaru 600. Yayin da yake halartar babban taron MDD a birnin New York, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya sanarwa duniya ikon mulkin kasar kan tsibiran Diaoyu. Ya ce,
"Tsibiran Diaoyu, yanki ne da kasar Sin ke mallaka!"