in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar kasar Lesotho a bikin EXPO na Shanghai
2010-10-04 17:26:13 cri

Daga nasa bangare kuma, Liu Jing, mataimakin ministan kare lafiyar al'ummar kasar Sin ya yi jawabin cewa, Litinin din nan, rana ce ta cika shekaru 44 da samun 'yancin kan kasar Lesotho, kuma kasar Sin na taya Lesotho murnar wannan muhimmiyar rana. Ya ce, zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu ya dade, musamman ma a cikin 'yan shekarun baya, kasashen biyu sun kara amincewa da juna ta fuskar siyasa, kuma sun samu kyawawan nasarori ta bangaren mu'amala da hadin gwiwar da ke tsakaninsu, haka kuma fahimtar juna da dankon zumunci ya karfafa tsakanin jama'arsu. Liu Jing ya kara da cewa, rumfar kasar Lesotho ta nuna mana yadda al'adun gargajiya da biranen zamani ke kasancewa tare da juna a kasar, haka kuma ta bayyana yadda jama'ar kasar ke fahimtar manufar "birane masu kayatarwa da zaman rayuwa mai inganci".

A gun bikin da aka yi wannan rana, 'yan wasa na kasar Lesotho sun sanya suturar gargajiya, sun kuma nuna wa jama'a wasanni masu ban sha'awa.(Lubabatu)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China