in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar kasar Lesotho a bikin EXPO na Shanghai
2010-10-04 17:26:13 cri

Ranar 4 ga wata rana ce ta rumfar kasar Lesotho a gun bikin baje kolin kasa da kasa da a halin yanzu ake yi a birnin Shanghai na kasar Sin. Sarkin kasar Lesotho, Letsie III, tare da mataimakin ministan kare lafiyar al'ummar kasar Sin, Liu Jing, sun halarci bikin murnar ranar.

Sarki Letsie III ya bayyana cewa, bayan wasannin Olympics da kasar Sin ta gudanar a shekarar 2008 a birnin Beijing, hedkwatar kasar, bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi a birnin Shanghai ya sake nuna karfin kasar wajen gudanar da manyan harkokin duniya, haka kuma ya bayyana muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa cikin harkokin duniya.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China