in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin birnin Wenzhou wadanda suke kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani
2010-09-13 15:45:32 cri

Garba: Ko da yake a kan shiga mawuyacin hali lokacin da kamfanonin kasar Sin suke neman damar shiga kasuwannin ketare, amma lokacin da aka samu matsalar hada-hadar kudi a duniya a shekarar 2008, kamfanonin birnin Wenzhou, kamar kamfanin kimiyya da fasaha na Tongling sun yi nasarar fama da kalubaloli iri iri. Mr. Chen Wusheng ya kara da cewa, "Yawan kayayyakin da ake bukata a kasuwa ya ragu sakamakon matsalar hada-hadar kudi, inda yawan masu sayen kayayyaki ya ragu. Amma ya kasance tamkar wani kamfanin kasar Sin, a ganina, wannan ne wata damar yin kasuwanci sabo da kayayyakinmu suna iya biyan bukatun da masu sayen kayayyaki suke da su. Alal misali, farashin kayayyakinmu da suke da inganci yana da rangwame. Wasu kamfanonin cinikayya na kasashen waje sun soma shigar da kayayyakinmu domin maye gurbin kayayyaki masu tsada da suka taba sayarwa a da."

Sanusi: Bayan da suka yi amfani da damar da ta bullo a kasuwa, yanzu dimbin kamfanonin da ke birnin Wenzhou sun soma zama kamfanonin fasahohin zamani a kai a kai. Mr. Chen Wusheng ya bayyana cewa, "Yanzu ana cikin zamanin yin kwan fitila irin na tsimin wuta. Idan ba a iya yin amfani da irin wannan kwan fitila na tsimin wuta bisa shiri ba, to, ba za a iya yin tsimin wuta kamar yadda ake fata ba. Yanzu muna samar da kayayyakinmu na tsimin wuta irin na musamman, bayan da aka yi amfani da su, za a iya kara damar yin tsimin. Haka kuma, yanzu a kan yi amfani da katakon waya a ofis, amma idan an zubar da ruwa a kan katakon waya irin na gargajiya nan take, na'urorin lantarki, kamar su kwamfuta da akwatin talibijin da aka hada su a wannan katakon waya za su lalace baki daya. Amma yanzu mun kirkiro wani sabon katakon waya don magance irin wannan matsala. Har yanzu babu wasu kamfanonin da suke iya samar da irin wannan katakon waya a duniya."

Garba: Yanzu, a kan samu sauye-sauyen tattalin arziki cikin sauri a duniya. Kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanonin dake birnin Wenzhou za su samu karin kalubaloli a nan gaba. Amma muna da imani cewa, za su samu sabon ci gaba kamar yadda ake fata bisa goyon bayan da gwamnatin kasar Sin ke nuna musu, da damar kasuwanci da suke samu. (Sanusi Chen)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China