Sanusi: A 'yan shekarun nan, irin wadannan kamfanoni masu zaman kansu dake birnin Wenzhou sun soma yin amfani da sabbin hanyoyi a kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani. A kwanan baya, wasu wakilan CRI sun ziyarci wasu kamfanonin dake birnin Wenzhou domin fahimtar yadda suke amfani da sabbin fasahohin zamani wajen fama da rikicin hada-hadar kudi da ya auku a duniya.
Garba: A shekarar 2008, wata matsalar ikon mallakar fasaha da ta auku a tsakanin wani kamfanin kasar Sin da wani na Amurka, kuma aka yanke hukunci kan na kasar Amurka ta jawo hankalin kasashen duniya sosai. A ran 10 ga watan Yuli na shekarar 2008, wata kotun kasar Amurka ta yanke hukunci da cewa, kamfanin kimiyya da fasaha na Tongling na kasar Sin ya yi nasara. Wannan ne karo na farko da wani kamfanin kasar Sin ya samu nasara cikin irin matsalolin ikon mallakar fasaha da ake yanke hukunci kansu a kasar Amurka.
Sanusi: An kafa kamfanin kimiyya da fasaha na Tongling na kasar Sin ne a shekarar 2001. Wannan kamfani yana samar da kayayyakin fasahohin zamani da yake da ikon mallakar fasaha domin fitar da su zuwa kasuwannin ketare. Mr. Chen Wusheng, shugaban hukumar direktocin wannan kamfani ya bayyana cewa, "Mu kan gamu da matsaloli kamar yadda sauran dimbin kamfanoni suke gamuwa da su lokacin da muke takara a kasuwannin ketare. Lokacin da muke sayar da kayayyakinmu a kasuwannin wasu kasashen waje, tabbas ne a dauki matakai iri iri domin hana shigarmu cikin kasuwanninsu. Sabo da haka, dole ne mu yi amfani da ikonmu na mallakar fasaha domin fama da irin wadannan matakai."