in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko zancen Muammar Gaddafi zai haifar da tasiri ga huldar da ke tsakanin Italiya da Libya
2010-09-01 16:52:55 cri

Duk da haka, Muammar Gaddafi, wanda kullum yake nuna halinsa na rashin furuci da ayyuka da ke firgita jama'a. A yayin ziyararsa, ya kwana ne cikin tantunan da ya je da su a maimakon shiga hotel, kuma ya kai ziyarar ne tare da masu gadi 40 da kuma wasu dawaki 30. Har wa yau kuma, a yayin ziyararsa ta tsawon kwanaki uku, ya yi jawabai biyu game da musulunci, inda ya ce, "bai kamata Turawa su bi Kirista ba, idan suna zabin addini, ya kamata su zabi musulunci. Ya kamata musulunci ya zama addinin da ake bi a nahiyar Turai baki daya."

To, hakan nan, kalaman tamkar sun sanyaya huldar da ke tsakanin kasashen biyu wadda ke kyautatuwa. Amma masu sharhi suna ganin cewa, ba za a samu manyan sauye-sauye ba ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Dalili kuwa shi ne, na farko, babban kamfanin man fetur na Italiya da aka sani da Eni yanzu ya kasance babban abokin hadin gwiwa na kamfanin man fetur mallakar gwamnatin Libya, kuma ban da wannan, yanzu kamfanonin Italiya na kokarin zuba jari a Libya, a yayin da Libya ke cin gajiyarsa. Na biyu , yalwata huldar da ke tsakanin kasashen biyu ya dace da moriyar kasar Italiya da kuma bukatunta. Lybia kasa ce da ke da arzikin mai da iskar gas a arewacin Afirka, a yayin da Italiya ta kasance kasar da ke fama da karancin makamashi, musamman ta fannin mai da iskar gas. A yayin da farashin mai ke tasowa a duniya, kyautata dangantakar da ke tsakaninta da Libya zai iya taimakawa wajen tabbatar da isashen mai da iskar gas ga kasar. Na uku, bunkasa dangantakarta da Italiya da kuma sauran kasashen yammaci ya dace da moriyar Libya. Ko da yake Libya tana da arzikin mai, amma sakamakon rashin ci gaban masana'antunta na hakar mai da karancin jari da fasahohi da kuma na'urori, tana bukatar kamfanonin man fetur na waje da su zuba mata jari ta bangaren hakar mai.

Yanzu haka, Italiya da Libya suna da abubuwan da suke bukata daga junansu, kuma suna son kara kyautata huldar da ke tsakaninsu, sabo da haka, mu'amalar da ke tsakaninsu ta fannonin siyasa da tattalin arziki za ta ci gaba. (Lubabatu)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China