Italiya ta taba shafe tsawon shekaru fiye da 30 tana mulkin mallaka a kasar Libya, kuma daga bisani, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta dade tana daskarewa. A karshen shekarun 1990, ta yin la'akari da moriyarta, Italiya ta yi kokarin neman kyautata huldarta da Libya. A shekarar 2008, kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar sada zumunta, inda Italiya ta amince da samar da dala biliyan 5 ga Libya cikin shekaru 20, a matsayin diyyar da ta biya kan mulkin mallaka da ta kafa a kasar da kuma kudin tsugunar da wasu bakin haure na Libya da Italiya ta turo su gida. Lallai yarjejeniyar ta bude wani sabon babi tsakanin kasashen biyu, har ma Italiya ta zama babbar abokiyar ciniki ta farko ga Libya, kuma kamfanonin Italiya suna kan wani muhimmin matsayi wajen harkokin hakar mai a Libya. A iya cewa, huldar da ke tsakanin Italiya da Libya na ta ci gaba zuwa wani sabon matsayi. Sabo da haka, a gun bikin da aka yi a ranar 30 ga watan da ya gabata, firaministan kasar Italiya, Silvio Berlusconi ya nuna babban yabo ga yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla, har ma ya bayyana Muammar Gaddafi a matsayin wani babban abokinsa.