Haka kuma, sabon tsarin mulki zai sa kaimi ga aikin raya tattalin arziki, musamman ma a kauyuka da masana'antu masu zaman kansu. Bisa sabon tsarin mulkin kasar, kananan hukumomin kasar za su samu kudin tallafi daga kudin harajin kasa da yawansu ya kai kashi 15 cikin 100, kuma wadannan kudade za su ba da tabbaci ga jama'a don su iya cimma daidaito wajen yin amfani da albarkatun kasar, da sa kaimi ga raya tattalin arziki na kauyuka da masana'antu masu zaman kansu na kasar, da rage matsin lamba da aka kawo wa birane manya da matsakaita sakamakon matsalar yunkurin raya birane
Haka kuma, bisa sabon tsarin mulkin kasar, idan dan kasa, wanda ke da gonaki da ba sa yin amfani, a ko wace shekara, dole ne mutumin ya biya kudin harajin kasa ga gwamnatin.
Wani jami'in da ke kula da cimma burin raya kasar Kenya na shekarar 2030 Muge Qbadi ya bayyana cewa, ta hanyar aiwatar da wannan sabon tsarin mulkin kasar, za a iya kara yin amfani da yankunan kasa, da kawo alheri ga jama'a, kuma za a kara samar da guraben aikin yi a kauyuka, da gaggauta raya tattalin arziki na yankunan karkara da yankunan masu talauci.
Haka kuma, a cikin sabon tsarin mulkin kasar, an ba da umurni game da matsalar zubar da ciki da ikon dokokin shari'a na Musulmi, inda aka bayyana cewa, likitoci na da ikon zub da ciki, idan rayuwar masu juna biyu tana fuskantar barazana, kuma kotun shari'a na da ikon warware matsalar, yayin da masu bin addini suka samu matsala game da aure da rabon gado da dai sauransu.
Jama'ar kasar Kenya suna sa rai sosai game da sabon tsarin mulkin kasar, kuma suna fatan za a kawo zaman lafiya da lumana da wadata a kasar Kenya, kuma ta hakan, kasar Kenya za ta kama hanyar farfadowa.(Bako)