An aiwatar da tsohon tsarin mulkin kasar Kenya a shekarar 1964, daga bisani kuma, an yi gyare-gyare har sau 7. Daga karshen shekarar 2007 zuwa farkon shekarar 2008, rikicin zabe ya barke a kasar Kenya, kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubun mutane, kana mutane kimanin dubu 350 sun rasa gidajensu. A karshen watan Afrilu na shekarar 2008, a karkashin shiga tsakani da kungiyar tarayyar Afrika ta yi, manyan jam'iyyun siyasa 2 na kasar Kenya sun cimma daidaito a tsakaninsu, kuma sun amince da kafa gwamnatin hadin gwiwa da kuma tsara sabon tsarin mulkin kasar. A ranar 4 ga watan Agusta na bana, jama'ar kasar Kenya sun jefa kuri'un raba gardama a kasar, don zartas da wannan sabon tsarin mulkin kasar.
Aiwatar da sabon tsarin mulkin kasar ya zamanto wani babban ci gaba da aka samu a cikin aikin yin gyare-gyare ga tsarin siyasa na kasar Kenya, a cikin sabon tsarin mulkin kasar, an kafa majalisar dattijai da babbar kotun koli ta kasar, kana an kawar da mukamin firaministan kasar, kuma an kayyade tare da sa ido kan ikon shugaba da mambobin majalisar ministoci ta kasar, haka kuma, sabon tsarin mulki ya yi umurni cewa, bai kamata 'yan majalisar dokoki sun zama manyan jami'an gwamnatin kasar ba. Duk wadannan matakan da aka dauka za su kawar da matsalar cin hanci da rashawa da matsalar rashin daidaito da ke kasancewa a cikin zamantakewar al'ummar kasar Kenya.
Haka kuma, a cikin sabon tsarin mulkin kasar, an kafa kananan hukumomi 47 a kasar, kuma an yi umurni ga ma'aikatun kasar da su rarraba iko gare su, ta hakan, kananan hukumomin kasar za su samu karin ikon shugabanci, ta yadda za a iya kara samun daidaito da kara raya kauyuka da kananan hukumomi na kasar.