in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sana'ar wayar salula ta zamani tana samun ci gaba a kasar Sin
2010-07-14 09:45:44 cri

Sanusi: Kasar Sin ta kirkiro sabon ma'aunin sabuwar fasaha irin ta zamani, wato ma'aunin TD-LTE da za a yi amfani da ita kan wayar salula. Mr. Zhao Zhongze, wanda ke kula da kasuwa a kamfanin Motorola ya bayyana cewa, kamfanin Motorola da kamfanin China Mobile, wato kamfani mafi girma a duniya wajen tafiyar da harkokin wayar salula sun riga sun kafa wani tsarin TD-LTE a rumfuna 7, ciki har da rumfar kasar Amurka da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai domin bayyana wa jama'a fasahar TD-LTE. Mr. Zhao ya ce, "A cikin wasu rumfuna, za a iya kallon shafin intanet kan wayar salula kai tsaye. Alal misali, za a iya yin amfani da katin TD-LTE domin kama kan shafin intanet kai tsaye. A kowace dakika, bayanai iri iri masu tarin yawa za su iya shiga wayar salula cikin sauri kwarai, har ma za a iya kallon wasu hotunan bidiyo kan wayar salula da yin hira ta bidiyo ko a yi taro irin na bidiyo ta wayoyin salula."

Ibrahim: Bikin EXPO na Shanghai da ake yi ya sa an kara saurin kyautata fasahar TD-LTE. Ya zuwa yanzu, kamfanoni da yawa sun riga sun samar da fasahohin yin amfani da wannan fasaha a kan wayar salula. Mr. Li Song, babban mai ba da shawara kan sashen kasuwanci na kamfanin Shanghai-Bell wanda ke karkashin kamfanin Alcatel-Lucent ya gaya wa wakilinmu cewa, kamfaninsa ya riga ya samar da shirin yin amfani da fasahar TD-LTE kan wayar salula domin nuna goyon bayan habakar fasahar TD-LTE, inda Mr. Li ya ce, "Bisa wannan sabuwar fasaha, za a iya gudanar da ayyuka da kallon shafukan bidiyo da hotuna bidiyo masu inganci kan wayar salula. Za mu aikewa da bayanai iri iri cikin sauri kwarai, wato masu yin amfani da wannan fasaha za su iya samun abubuwa masu inganci sosai a kan wayar salularsu."

Sanusi: An bayyana cewa, yanzu kamfanin China Mobile yana kara saurin gina kananan tasoshi wadanda suke goyon bayan fasahar zamani irin ta zamani na uku. A nan gaba, za a iya ci gaba da kyautata wadannan tasoshi domin nuna goyon bayan tsarin TD-LTE. Mr. Wang Jianzhou, shugaban kamfanin China Mobile ya bayyana cewa, kamfaninsa zai samar da karin kananan tasoshi a duk fadin kasar. (Sanusi Chen)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China