Sanusi: Ya zuwa watan Afrilu na bana, yawan mutanen da suke amfani da wayar salula ya kai miliyan 786 a kasar Sin. Mr. Shi Xiansheng, mataimakin babban sakataren kungiyar shafin intanet ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu yawan mutanen da suke amfani da wayar salula domin kama shafin intanet ya wuce wadanda suke amfani da shafin intanet ta hanyar yin amfani da na'urorin kwamfuta. Kuma kasar Sin tana shiga lokacin bunkasa shafin intanet ta wayar salula. Mr. Shi ya bayyana cewa, "Sana'ar shafin intanet za ta shiga lokacin samun bunkasuwa ta hanyar yin amfani da wayoyin salula, wato za a iya kafa wani tsarin shafin intanet ta wayoyin salula, inda za a iya samun muhimman bayanai da yin cinikayya da sauraron wake-wake da dai sauransu."
Ibrahim: Yanzu, ana iya aikewa da sakwanni da hotuna masu launuka, da karanta labaru, har ma a kalli bidiyo ta wayar salula. Ana shakkar cewa, mene ne irin wadannan sabbin fasahohin wayar salula za su haifar mana a nan gaba? Mr. Xu Hao, babban injiniya na kamfanin "Qualcomm Incorporated" wani kamfanin nazarin fasahohin sadarwa na kasar Amurka, ya bayyana wa wakilinmu cewa, "Bambancin da ke tsakanin fasaha irin ta zamanin farko zuwa na biyu shi ne ana amfani da fasahar rubuta bayanai ta wayar salula irin ta zamani na biyu. Amma bambancin da ke tsakanin zamani na biyu da na uku shi ne saurin aikewa da bayanai ta wayar salula. Bisa sabuwar fasaha, za a iya aikewa da bayanai iri iri ta wayar salula cikin sauri kwarai."