in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daukar nauyi tare kuma jin dadin makoma tare
2010-07-02 17:17:18 cri

Ya kamata mu kyautata hanyar neman bunkasuwa domin sa kaimi ga bunkasuwar birane mai dorewa. "Yarjejeniyar Kyoto", da taron sauyawar yanayi da aka yi a Copenhagen, da bikin EXPO na Shanghai sun fadakar da jama'a cewa, hanyoyin neman bunkasuwa da amfani da makamashi maras gurbata yanayi zai sa kaimi ga bunkasuwar birane da tattalin arziki yadda ya kamata.

Ya kamata birane su hada kansu domin neman moriyarsu tare. Batun kiyaye muhalli ba aiki ne na wani birni kawai ba, kuma babu wani birni da zai iya warware matsalar muhalli da kansa. Dole ne kasa da kasa su yi hadin gwiwa a manyan fannoni, kuma ana bukatar taimakon juna tsakanin birane. Bai kamata kasashe masu tasowa su sake neman bunkasuwar masana'antu kamar yadda kasashe masu ci gaba suka yi ba, kuma dole ne kasashe masu ci gaba su dauki nauyi ba da taimakon fasaha da taimakon kudi ga kasashe masu tasowa. Idan kasashe maso tasowa da masu ci gaba suka hada kansu ba makawa, za a iya warware matsalar muhalli da bil Adam ke fuskanta.

Ya kamata birane su bunkasa tattalin arzikin ba tare da abubuwan da ke gurbata muhalli ba. Yanzu kasar Sin na kokarin bunkasa birane, tare da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kuma ta yi alkawari cewa, yawan iskar da ke dumama yanayi da za ta fitar a shekarar 2010 zai ragu da kashi 40 zuwa kashi 45 bisa na shekarar 2005.

Sakamakon bikin EXPO na Shanghai, kasar Sin ta sami damar koyon ilmin kiyaye muhalli da yin tsimin makamashi daga birane masu ci gaba na kasashen duniya. Mun gaskata cewa, idan kasashe suka aiwatar da manufofin neman bunkasuwa ta hanyar kiyaye muhalli, kamfannoni su kera kayayyaki ta hanyar yin tsimin makamahi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, suma mazauna su tafiyar da harkokinsu ta hanya maras gurbata muhalli, hakika za mu sami wata kyakkyawar makoma a birane. (Musa Guo)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China