in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daukar nauyi tare kuma jin dadin makoma tare
2010-07-02 17:17:18 cri

A zamanin yau, bil Adam yana fuskantar matsalar muhalli yayin da ake kokarin bunkasa masana'antu, musamma ma a birane. Saboda haka, a lokacin bayan watanni biyu da bude bikin EXPO na Shanghai, an shirya wani dandalin tattaunawa mai taken "matsalar muhalli da nauyin da ke kan birane". Jami'an gwamnati, kwararru da masana ilmi, da masu masana'antu na kasashe daban daban za su tattauna sosai kan matsalar muhalli domin samu ra'ayi daya, da gabatar da hanyoyin tinkarar wannan matsala.

Yin tattaunawa kan nauyin kiyaye muhalli ya nuna cewa, bil Adam yana nuna nadama ga tabarbarewar muhalli. Bil Adam ya sami ci gaba sosai a cikin shekaru 150 da suka wuce, amma ya lalata muhallin duniya sosai. Ya kamata birane su dauki nauyin matsalar da ke shafar muhalli, kuma matsalar muhalli tana yin tasiri ga moriyar birane. Dole ne gwamnatoci, da kamfannoni, da mazauna su hada kansu su yi kokari tare domin kiyaye muhalli, da tinkarar sauyawar yanayi da kuma yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli.

Kasar Sin wata kasa ce mai tasowa, kuma tana kokarin neman bunkasuwa ta hanyar kimiyya kuma mai dorewa. Shugaba Hu Jintao ya taba yin nuni da cewa, "Dole ne a gudanar da manufar yin tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli, wannan ya shafi moriyar jama'a da makomar al'ummar Sin. Dole ne a yi kokarin gina wani tsarin zaman al'umma mai tsimin makamashi, da kyakkyawan muhalli." Yayin da kasar Sin ke raya tattalin arziki, ba za ta canja manufarta na kiyaye muhalli ba, kuma wannan nauyi ne na dukkan birane, da kamfannoni, da sauran mutane.

Babban taken bikin EXPO na Shanghai shi ne "Birni mai kayatarwa da zaman rayuwa mai inganci", wannan ya nuna cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashe daban daban domin tinkarar matsalar muhalli, da daukar wannan nauyi yadda ya kamata.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China