A lokacin da Eriksson yake magana kan yadda kasashe 6 na Afirka suka yi a gasar cin kofin duniya a wannan karo, ya nuna mamakinsa, bai san dalilin da ya sa 'yan wasan Afirka ba su nuna ainihin karfinsu ba. Amma ya tuna wa mutane cewa, 'yan wasan Afirka sun fita daga gasar ce tare da samun girmamawa. Akwai 'yan wasa masu tarin yawa a nahiyar Afirka, wadanda Allah ya ba su baiwar wasan kwallon kafa. Eriksson ya yi imani da cewa, yanzu 'yan wasa da yawa daga cikin kasashe 6 da suka shiga gasar ta Afirka ta Kudu za su sake bayyana a gasar cin kofin duniya.
Haka zalika kuma, Didier Drogba, babban tauraron wasan kwallon kafa na Kodivwa ya kasance wanda ya fi yin fice a karawar da aka yi tsakanin Kodivwa da Korea ta Arewa. A karawar share fagen gasar cin kofin duniya da aka yi a farkon watan Yuni, ya karya hannunsa, duk da haka a Afirka ta Kudu, ko da yake bai warke sosai ba, amma ya shiga gasar, inda kuma ya ba da gudummawa sosai. Gaza tsallakewa zuwa zagaye na 2 a gasar cin kofin duniya da Kodivwa ta sake yi ya bata ransa kwarai, inda ya ce,"A ganina, mun samu sa'ar shiga gasar cin kofin duniya har sau 2. Shiga gasar cin kofin duniya har sau 2 yana da matukar kyau ga kasarmu ta Kodivwa. Kuma karawa da Brazil da Portugal, wadanda kowa ya san kasashe ne masu karfi, buri ne ga kasarmu, mun taki sa'a. Sa'an nan kuma, mun yi farin ciki da karawa da kasashe masu karfi a wasan kwallon kafa."(Tasallah)