in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kodivwa ta sanya fata kan gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil
2010-06-30 13:30:52 cri

Ko da yake a karawa ta karshe a cikin rukuni na 7 a gasar cin kofin duniya, kasar Kodivwa ta lallasa kasar Koriya ta Arewa da ci 3 da nemaa ran 25 ga watan Yuni, amma dukkansu sun rasa damar tsallakewa zuwa zagaye na 2.

Duk da haka, Sven Goran Eriksson, mai horas da 'yan wasan Kodivwa, kuma dan kasar Sweden yana ganin cewa, a karawa guda 3 cikin rukuni na 7 a gasar, hakika 'yan wasan Kodivwa sun gamu da wasu matsaloli, amma suna da gwaninta, suna iya wasa tare, sun iya samar da zarafin zura kwallon cikin ragar abokan karawa. Haka kuma, Kodivwa tana fuskantar kyakkyawar makoma a fagen wasan kwallon kafa. Eriksson ya ce,"Ina farin ciki matuka da ganin wannan kungiya tana kara kyautata a kai a kai. Ko wane dan wasan na samun kyautatuwa, haka kuma, suna iya wasa tare, mun iya ganin ci gabansu a karawar da suka yi. A karawar da suka yi a tsakaninsu da Brazil, ba su iya mai da hankali sosai kan karawar ba, sun dan gaji, Brazil ta zura kwallo a ragarmu cikin sauri. Amma baya ga wannan, 'yan wasan Kodivwa suna da kyau, sun bi umurnina, suna son yin aiki tukuru. Ina jin dadin kasancewa da su a makonni da dama da suka wuce. Suna da kyau, kuma suna wasa cikin farin ciki."

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China