in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba da shawarar kafa tsarin kudi da zai iya taimakawa kokarin raya masana'antu
2010-06-28 14:54:21 cri

Lokacin da yake tabo bayani kan yadda za a ci gaba da yin kwaskwarimar hukumomin kudi na kasa da kasa, Hu Jintao ya ce, dole ne a kara saurin daidaita kason asusun ba da lamuni na kasa da kasa, wato IMF domin yawan mutane a kasashe masu tasowa da za su iya samun muhimman mukamai a hukumomin kudi na kasa da kasa zai iya karuwa. Sabo da haka, kasashe masu tasowa za su iya samun karin ikon wakilci da ikon ba da ra'ayoyinsu cikin wadannan hukumomi. Sannan ya kamata a kyautata karfin asusun ba da lamuni na kasa da kasa da kuma sa ido kan yadda yake tafiyar da ayyukansa. Bugu da kari, ya kamata a kara sa ido kan manufofin raya tattalin arziki da bangarori daban daban, musamman muhimmin bangare wanda ke samar da adanannun takardun kudin ajiya a duniya suke bi.

Hu Jintao ya jaddada cewa, cimma burin raya tattalin arziki mai inganci cikin daidaito ba tare da cikas ba wani aiki ne mai sarkakiya da zai kasance a duniya cikin dogon lokaci mai zuwa, ba zai yiwu a cimma wannan buri nan da nan ba. Dole ne a tsaya tsayin daka kan matsayin kokarin cimma wannan buri cikin dogon lokaci mai zuwa.  (Sanusi Chen)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China