in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba da shawarar kafa tsarin kudi da zai iya taimakawa kokarin raya masana'antu
2010-06-28 14:54:21 cri

A ran 27 ga wata an yi taron koli a karo na 4 na shugabannin mambobin kungiyar G20 a birnin Toronto na kasar Canada. A gun taron, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi wani muhimmin jawabi mai taken "Hada kan juna domin kafa wata kyakkyawar makoma", inda Mr. Hu ya bayar da ra'ayoyinsa game da halin da ake ciki a fannin tattalin arziki da fatansa na gyara ka'idojin kungiyar G20. Haka kuma, ya bayar da ra'ayoyi 3 kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa mai inganci kuma cikin daidaito ba tare da cikas ba ko bata lokaci ba. Bugu da kari, ya ba da shawara cewa, ya kamata a kafa wani tsarin kudi da zai iya taimakawa masana'antu. Sannan, Mr. Hu ya jaddada maganar neman ci gaba, inda ya ce, kungiyar G20 tana da hakkin samar da karin albarkatun tattalin arziki da nuna goyon baya a fannin siyasa domin daidaita batun neman ci gaba.

Taron koli na shugabannin mambobin kungiyar G20 da aka yi a Toronto, shi ne taron farko da aka yi bayan da aka tabbatar da cewa kungiyar G20 dandali ne mafi muhimmanci wajen tattauna batun tattalin arzikin kasa da kasa, kuma an yi wannan taro ne a daidai lokacin da ake kokarin farfado da tattalin arzikin kasa da kasa.

A cikin jawabinsa, Hu Jintao ya bayar da ra'ayoyi 3 kan yadda za a raya tattalin arzikin kasa da kasa cikin daidaito ba tare da cikas kuma cikin hanzari, inda Mr. Hu ya ce, akwai bukatar a yi kokarin mayar da nauyin yakar rikicin hada-hadar kudi da ke bisa wuyan kungiyar G20 ya zuwa wani muhimmin dandalin yin hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa. Kuma a kafa wani sabon tsarin hada-hadar kudi da ake iya bin wannan tsari cikin zaman daidai wa daida da adalci da oda. Haka kuma a kafa tsarin cinikayya da ake iya dogara a kai domin yin ciniki cikin 'yanci.

Hu Jintao ya kara da cewa, ya kamata a kara sa ido kan hukumomin tabbatar da amana, kuma kada a dogara da su a kullum, sannan ya kamata a kyautata ka'idojin sa ido kan hukumomin tabbatar da amana domin kafa wata hanya da ma'auni mai dacewa. Sabo da haka, sakamakon da hukumomin tabbatar da amana suka bayar zai iya bayyana hakikanin halin da kowace kasa ke ciki a fannin tattalin arziki, kuma za su iya samar da daidai matsayin da amanar kowace kasa ko wata hukumar tattalin arziki ke dauka.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China