in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a birnin Shanghai
2010-04-21 10:46:45 cri

Bayan da ka ci kasuwa, kada ka matan ka je "filin Xin Tiandi", wani sabon wurin shan iska. Gine-ginen da aka gina a wannan fili sun yi kama da salon gargajiya na gine-ginen Shanghai. A wannan wuri, za ka shakata da kuma sanin mene ne al'adun birnin Shanghai.

Ko da yake birnin Shanghai birni ne da ke nuna al'adun zamani sosai, amma a hakika dai, akwai abubuwan tarihi da suke kasancewa a birnin. Sabo da haka, zango na uku da za mu je yau shi ne lambun shan iska mai suna "Yu Yuan", inda ke nuna al'adun yankin da ke kudu da kogin Yangtze. Yau fiye da shekaru 450 da suka gabata ne wani mai arziki ya gina wannan babban gidan nasa na "Yu Yuan". Yanzu, akwai dimbin littattafai da kayayyakin gida da kayayyakin fadi-ka-mutu da aka adana a cikin wannan farfajiya. Sannan wani wuri daban da ke dab da "Yu Yuan" shi ne "dakin ibada na Chenghuang", wato wani dakin ibada na addinin Taoist, wani addinin gargajiya na al'ummar Sinawa. A kan fadi cewa, lokacin da kake ziyara a birnin Shanghai, idan ba ka je wannan dakin ibada na Chenghuang ba, za a ce, ba ka kai ziyara a birnin ba. Ka ga matsayin da wannan dakin ibada na Chenghuang yake da shi a birnin Shanghai, kuma tasirin da yake yi wa birnin.

To, masu sauraro, yanzu bari in gabatar muku tambayoyi guda biyu na yau. Tambaya ta farko, wane wuri ne da ake kira layin da ke nuna alamar siga birnin Shanghai? Tambaya ta biyu ita ce, wane titi ne ake kira "titin kasuwanci na farko a kasar Sin" a birnin Shanghai? Jama'a masu sauraro, muna jiran amsoshinku ta wannan adirishi:

China Radio International

PMB 758

Garki, Abuja, Nigeria

(Sanusi Chen)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China