Zangon farko da za mu je shi ne "Waitan" wuri ne da fadinsa ya kai kimanin murabba'in kilomita 1.5, kuma ya yi suna sosai a kasar Sin. Wannan wuri dake yammacin kogin Huangpu, wato kogi ne da ya ratsa birnin Shanghai, yana da manyan gine-gine fiye da 50 da sigoginsu da suke bayyana al'adun kasashen duniya. Sabo da haka, ana kiran wadannan gine-ginen da ke "Waitan" da sunan layin da ke nuna alamar siga birnin Shanghai. Sannan, birnin Shanghai ya kasance tamkar wata babbar kasuwa, wato kyakkyawan wuri ne da masu sayayya suke son zuwa. Lokacin da ka je birnin Shanghai, idan har ba ka ci kasuwar garin ba, hakika za ka yi da-na-sani. Sabo da haka, zango na biyu da za mu je shi ne titin Nanjing, inda ke da dimbin tsoffin kantuna da sabbin kantunan zamani da dai makamatansu. Ba ma kawai akwai dimbin kayayyakin da samari da 'yan mata suke son saya ba, har ma akwai dimbin kananan kantunan sayar da kofi da kayan tande-tande da lashe lashe iri iri. A gefen titin Nanjing, akwai bishiyoyin Phoenix da wasu kananan lambunan shan iska da wasu mutum-mutum masu ban sha'awa da dimbin kayayyakin da aka zana hotunan "Hai Bao" da sauran zane-zane. Sabo da haka, ana kiran titin Nanjing na birnin Shanghai "titin kasuwanci na farko a kasar Sin"