in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da Jia Qinglin ya yi a Afirka ta samu sakamako sosai
2010-04-02 21:29:23 cri

Wang Shenghong ya bayyana cewa, a yayin ziyarar, Mr.Jia Qinglin ya yi kokarin bayyana wa jama'ar kasashen uku yanayin da Sin ke ciki da kuma hanyoyinta na samun ci gaba da manufofin da ta dauka ta fannin diplomasiyya da harkokin Afirka, wadanda suka sami martani sosai daga bangarori daban daban. Jia Qinglin ya kuma yi hira da manyan gidajen telebijin da jaridu na kasashen uku, inda ya yi cikakken bayani game da manufofin Sin kan kasashen Afirka da kuma mayar da amsa kan shakkun da kasa da kasa ke nunawa kan wasu batutuwa, tare da yin watsi da kalamai na wai "barazanar Sin" da "sabon mulkin mallaka da Sin ta kafa", wanda kuma ya shaida wa duniya kasancewar Sin babbar kasa mai son zaman lafiya da ci gaba da yin hadin gwiwa. Bayan haka, Jia Qinglin ya yi musayar ra'ayoyi tare da jama'ar kasashen uku da suka fito daga bangarori daban daban, domin isar da zumuncin jama'ar kasar Sin a gare su. Jama'ar kasashen uku suna ganin cewa, ziyarar da Jia Qinglin ya kai musu ta kara fahimtar da su hanyar da kasar Sin ke bi wajen samun ci gaba da manufofin kasar na cikin gida da na waje, haka kuma ta kusantar da su ga jama'ar Sin da kuma inganta imaninsu na karfafa hadin gwiwa da juna.

Wang Shenghong ya ce, ziyarar da Mista Jia ya kai wa nahiyar Afirka ta kara kyautata hadin gwiwar dake gudana a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, sa'an nan ta kara sanya wasu abubuwa a sabon tsarin huldar abota ta manyan tsare-tsare da ke tsakanin bangarorin 2. Wani babban aikin da Mista Jia ya dauki niyyar aiwatarwa a lokacin ziyararsa shi ne inganta hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Kamaru, Afirka ta Kudu, da kuma Namibiya. Shi ya sa Mista Jia ya gabatarwa shugabanni da masu masan'antun kasashen 3 yadda kasar Sin take kokarin raya tattalin arzikinta, haka kuma ya halarci tarurrukan da suka hada da 'dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka ta Kudu dangane da hadin kai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya', da 'taron yin hira da wakilan masana'antun kasar Sin da ke gudanar da ayyukansu a kasar Afirka ta Kudu', da dai makamantansu. A wajen bukukuwan da aka shirya masa, Jia Qinglin ya bayyana cewa, kasashen Afirka da kasar Sin za su iya rufa wa juna baya ta hanyar hada kawunansu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Kasar Sin za ta aiwatar da alkwarin da ta yi na daukar matakai 8 don neman habaka hadin kai da ke gudana a tsakanin bangarorin 2, ta yadda za a iya taimakawa kasashen Afirka don su kyautata zaman rayuwar jama'a, da kara samun damar raya kasa bisa karfinsu, da kuma samar da bunkasuwa mai dorewa. A karshe dai za a sa kasashen Afirka da kasar Sin dukkansu samun moriya da yawa. (Tasallah Yuan / Lubabatu Lei / Bello Wang)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China