A kan hanyarsa ta dawowa kasar Sin, Wang Shenghong, mataimakin sakataren majalsar CPPCC ya yi wa manema labaru bayani kan ziyarar. A ganinsa, ziyarar da Mr. Jia Qinglin ya yi a Afirka na matsayin muhimmin matakin diplomasiyya ne da kasar Sin ta dauka domin aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka daga dukkan fannoni da sa kaimi kan raya huldar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da kasashen Afirka bisa manyan tsare-tsare. Haka kuma, ziyarar na da muhimmiyar ma'ana a fannonin zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da kasashen 3 da inganta hadin gwiwa da hada kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Mr. Wang ya kara da cewa, a lokacin ziyararsa, Mr. Jia Qinglin da shugabannin kasashen 3 sun sami ra'ayi daya kan raya hulda a tsakanin Sin da kasashensu da kyautata hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, hakan ya inganta hulda a tsakanin Sin da kasashen 3 da kuma kafa harsashin siyasa a tsakanin Sin da Afirka wajen bunkasa zumuncinsu.