in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da Zambia ke ciki a fannin bunkasuwar fasahar aikin sadarwa
2010-01-28 17:11:40 cri

Sa'an nan kuma, Mr. Makuni ya gabatar da wasu misalai. Yanzu a Zambia, mutane kimanin dubu 18 kawai suka yi rajistan yin amfani da yanar gizo ta Internet, amma jimillar mutanen wannan kasa ta kai miliyan 11 gaba daya. Ban da wannan kuma, Zambia ba ta kafa babban tsarin Internet na zamani irin na Optical fiber ba tukuna, jama'ar kasar na dogara da tauraron dan Adam domin yin amfani da Internet, ta haka kudin yin amfani da Internet na da tsada matuka, kuma saurin Internet cikin nawa ne yake kasancewa. Yawan kudin da a kan kashe domin yin amfani da Internet a wata guda ya kai daruruwan dalar Amurka, wannan ya hana masu sayayya su yi amfani da Internet.

Duk da haka, a ganin Makuni, ba da hidimar aikin sadarwa na samun saurin bunkasuwa a wannan kasar da ke kudancin Afirka. Mutane kimanin miliyan 3 suna samun hidimar da kamfanin gudanar da harkokin aikin sadarwa mafi girma a Zambia wato Zain-Zambia suke bayarwa. Sa'an nan kuma, kamfanin MTN, wanda girmansa ya zama na 2 a Zambia yana ba da hidima ga mutane miliyan 1 da dubu 500. Haka zalika, bunkasuwar aikin sadarwa ta sa kaimi kan wasu sana'o'in da suka shafa harkokin kudi sun samu ci gaba sosai. Hakan yana nan yana canza hanyoyin da Zambia take bi wajen ba da hidimar kudi.

Mr. Makuni ya ce, ko da yake jama'ar Zambia ba su yi amfani da Internet kwarai da gaske ba, amma gwamnatin Zambia tana yin gwajin gudanar da ayyukanta ta hanyar Internet. Yanzu gwamnatin ta riga ta fara kafa babban tsarin Internet na zamani irin na Optical fiber da zummar canza halin da kasar ke ciki a fannin aikin sadarwa daga dukkan fannoni.(Tasallah)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China