in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da Zambia ke ciki a fannin bunkasuwar fasahar aikin sadarwa
2010-01-28 17:11:40 cri

Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin cikin shirinmu na Afirka a Yau. A cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku da halin da kasar Zambia take kasancewa a fannin bunkasuwar fasahar aikin sadarwa yanzu haka.

A kwanan baya, Milna Makuni, wani kwararre mai ilmin fasahar aikin sadarwa na kasar Zambia ya yi wa manema labaru na kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin bayani da cewa, a sakamakon kashe kudi da yawa, ya zuwa yanzu a baya ne kasar Zambia take kasancewa a fannin fasahar aikin sadarwa, in an kwatanta ta da wasu kasashen Afirka. Amma a bayyane ne sana'ar sadarwa irin ta wayar salula na samun saurin bunkasuwa a wannan kasar da ke kudancin Afirka. Yanzu gwamnatin Zambia ta riga ta fara kafa tsarin Internet na zamani irin na Optical fiber, da zummar kyautata halin da kasar take kasancewa ta fuskar aikin sadarwa daga dukkan fannoni.

Mr. Makuni ya kara da cewa, a matsayinta ta daya daga cikin kasashen da ake biyan kudi da yawa domin samun takardar iznin ba da hidimar aikin sadarwa da kuma rashin isassun na'urorin aikin sadarwa, a halin yanzu kasar Zambia tana ba da hidimar da abin ya shafa a wasu muhimman birane kawai. A yankunan karkara, ba ta fara ba da hidimar fasahar zamani tukuna ba. Wannan kasar da ke kudancin nahiyar Afirka tana Alla-Alla wajen rage kudin kaddamar da hidimar aikin sadarwa domin raya tattalin arziki. Mr. Makuni ya taba rike mukamin babban sakataren hukumar masu hikima ta Zambia wato "e-Brain", wadda ke bai wa gwamnatin kasar shawara.

Mr. Makuni ya yi bayani da cewa, bisa sabon binciken da Bankin Duniya ya yi, an ce, kudin da ake kashewa domin buga waya a tsakanin kasa da kasa a kasar Zambia ya fi tsada a duk kudu maso gabashin Afirka. Yawan kudin da kamfanonin ba da hidimar aikin sadarwa su kan kashe domin shiga tsarin buga wayar tarho a tsakanin kasa da kasa ya kai dalar Amurka miliyan 12. Wannan ya damu kamfanonin sosai, haka kuma, kamfannonin sun rarraba irin wannan kudin da tilas ne su kashe domin ba da hidima kan ko wane mai sayayya. Mr. Makuni ya ce, yawan irin wannan kudi ya kai dalar Amurka dubu 214 a kasar Kenya, a kasar Uganda kuma, yawan irin wannan kudi ya kai dalar Amurka dubu 50 kawai.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China