Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-17 15:03:06    
Masu aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing a filin jirgin saman Beijing

cri

Li Jianxin ta ce, ta dade tana aiki a sashen bayar da bayanai na filin jirgin saman Beijing, shi ya sa ta fahimci yadda ake tafiyar da ayyuka daban-daban na filin jirgin saman kwarai da gaske. Ko da yake ta tsufa, wasu lokuta ma za ta ji gajiya yayin da take aiki, amma a duk lokacin da take bayar da taimako ga sauran mutane, tana farin-ciki sosai. Ta ce:

"Yayin da nike kokarin bayar da taimako ga sauran mutane, musamman ma ga wasu nakasassu ko tsofaffi, na taimake su wajen shiga mota ko daukar kayayyakinsu, na ji matukar farin-ciki."

Tare da karatowar gasar wasannin Olympics ta Beijing, an fara gudanar da aikin bada tabbaci ga zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin saman Beijing tun daga ranar 1 ga watan Yuli. Zuwa ranar 30 ga watan Satumba, adadin mutane masu aikin sa-kai a filin jirgin saman Beijing zai kai 2000, kuma za su gudanar da aikinsu har na tsawon awoyi 24 a kowace rana. Wadannan masu aikin sa-kai za su taimaki 'yan wasan motsa jiki, da jami'ai, da manema labaru daga kasashe da wurare daban-daban na duniya, wajen tafiyar da ayyuka daban-daban, da warware matsalolin ba-zata da dai sauransu.


1 2 3 4 5