Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-17 15:03:06    
Masu aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing a filin jirgin saman Beijing

cri

A matsayin wata daliba wadda har yanzu ba ta gama karatunta ba a jami'a, wani lokaci, Gong Chen ta ji gajiya bayan da ta yi aikin sa-kai a filin jirgin saman Beiing, amma ta ce, ta ji matukar farin-ciki a duk lokacin da ta amsa tambayoyin da fasinjoji suka yi mata. Yayin da take zantawa da abubuwan da ta samu daga aikin sa-kai a filin jirgin sama, ta fadi cewa, aikin nan ba ma kawai zai kyautata harshen Faransanci nata ba, hatta ma zai inganta kwarewarta wajen yin mu'amala da cudanya da mutane daban-daban. Wannan aiki zai kasance wata babbar dukiya a cikin duk rayuwarta.

A kofar shiga dake sashe na 2 na filin jirgin saman Beijing, wata gyatuma dake saye da rigar aikin sa-kai ta jawo hankalin wakilinmu. Tana kaiwa da kawowa tsakanin sashen amsa tambayoyin fasinjoji da kofar shiga ta filin jirgin sama ba tsare da tsayawa ba, wani lokaci ta amsa tambayoyi daban-daban da fasinjoji suka yi mata, wani lokaci kuma ta taimaki wasu fasinjoji nakasassu wajen daukar kayayyakinsu. Sunan wannan gyatuma shi ne Li Jianxin, wata ma'aikaciya ce ta sashen bayar da bayanai na filin jirgin saman Beijing. Madam Li, 'yar shekarun 58 da haihuwa, za ta yi ritaya nan da shekaru biyu masu zuwa. A halin yanzu, za'a kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing nan ba da jimawa ba, kuma aikin bada tabbaci ga zirga-zirgar jiragen sama yadda ya kamata a filin jirgin saman Beijing ya yi yawa sosai, shi ya sa madam Li ta yi rajistar zama wata mai aikin sa-kai, domin bada taimako ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. A cikin lokacin hutunta, ta kokarta ba tare da kasala ba wajen bayar da hidima ga fasinjoji da dama. Ta ce:

"Karbar bakuncin gasar wasannin Olympics, wani mafarki ne da Sinawa suke neman cimmawa a cikin shekaru da dama. A ganina, shirya gasar wasannin Olympics zai haifar da zaman wadata ga kasarmu. Nan da shekaru 2 masu zuwa, zan yi ritaya. A ganina, aikin sa-kai ga gasar wasannin Olympics ta Beijing na da babbar ma'ana gare ni, musamma ma bayan da na yi ritaya, idan na waiwayi wannan aiki, ko shakka babu zan yi farin-ciki sosai."


1 2 3 4 5