A cikin 'yan kwanakin da Gong Chen ke aiki a filin jirgin saman Beijing, ta ji damuwar da wasu fasinjojin suka nuna yayin da suke yin tambayoyi. Ta ce:
"Abin da ya fi burge ni shi ne, yayin da mutane suke daukar jirgin sama a karo na farko, zuciyarsu yana dar-dar, har ma ba su san yadda za su yi ba. Akwai wani fasinja wanda ya tambaye ni,'Ina matakala take?' Na amsa cewa, 'Tana bayanka.' Daga baya dai ya tambaye ni, 'ina baya yake?'"
Gong Chen ya gayawa wakilinmu cewa, a matsayin wata daliba mai koyon harshen Faransanci, tana son bada hidima ga wadanda ke magana cikin Faransanci. Amma, yayin da take fuskantar fasinjoji daban-daban daga kasashe daban-daban wadanda yarensu ko lafazinsu na Faransa ya sha bamban, Gong Chen ta ji matsin lamba sosai. Ta ce:
"Saboda irin harshen Faransanci da fasinjoji daga kasashen Afirka suke magana ya sha bamban da na harshen Faransanci na Faransa, shi ya sa wasu lokuta kamata ya yi in yi magana cikin daidaitaccen Faransanci, wasu lokuta kuma sai Faransanci na Afirka, wasu lokuta sai Turanci, lalle na sha wahala kadan."
1 2 3 4 5
|