Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-17 15:03:06    
Masu aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing a filin jirgin saman Beijing

cri

Wannan yarinya mai aikin sa-kai wadda ke amsa tambayar da fasinja ya yi mata, sunanta Gong Chen, wadda ke koyon harshen Faransanci a sashen koyon harsunan waje na kwalejin birni a Beijing. Watanni uku da suka gabata, Gong Chen ta yi rajista sa'annan ta ci jarrabawa iri-iri, a karshe dai ta zama wata mai aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing a filin jirgin saman Beijing. Babban nauyin da aka danka mata shi ne, amsa tambayoyin da fasinjoji suka yi mata, da zama mai fassara ga mutanen da suka zo daga kasashe wadanda suke magana cikin harshen Faransanci. Yayin da take tabo magana kan dalilin da ya sa ta zabi zama wata mai aikin sa-kai a filin jirgin sama, ta ce:

"A ganina, zama wata mai aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics wani babban aiki ne gare ni. Haka kuma, Sinawa suna nan suna jira har na shekaru da dama, a karshe dai sun sami wannan dama wajen shirya gasar wasannin Olympics a Beijing. Ina tsammani wannan shi ne wani muhimmin zarafi gare ni. Kazalika kuma, na iya kyautata harshen Faransanci nawa yayin da nike aikin sa-kai a nan filin jirgin saman Beijing."

Watakila ma kuna tsamanin cewa, aikin amsa tambayoyin da fasinjojin suka yi na da sauki sosai. Amma a gaskiya dai, wannan shi ne wani jan aiki ne ga mutane masu aikin sa-kai wadanda ba su taba tafiyar da aiki a filin jirgin sama a lokacin da ba. Aikin nan ya bukaci masu aikin sa-kai da su rike yadda ake tafiyar da aiki a wuare daban-daban na filin jirgin saman Beijing sosai a cikin zuciya, da bayar da hidima ga fasinjojin da suke kaiwa da kawowa a tsanake kuma tare da cikakken zafin-nama.


1 2 3 4 5