A cikin shirinmu na yau, za mu sanya muku wani bayani dangane da matasa masu aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing, da ayyukan da suke yi ba ji ba gani. Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, an riga an kammala aikin tattara dubun-dubatar mutane masu aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing daga wurare daban-daban na kasar Sin, a halin yanzu, bi da bi ne wadannan masu aikin sa-kai suka fara gudanar da ayyukansu. A filin jirgin saman Beijing, ana iya ganin mutane masu aikin sa-kai a ko'ina, wadanda suke saye da tufafin T-Shirt masu launin ja iri daya, suna kokarin bayar da kyakkyawar hidima ga fasinjojin da suke kaiwa da kawowa.
Wani fasinja ya ce: "Sannunki! Don Allah, ina so ki gaya mini yaushe ne wannan jirgin sama zai iso? Na gode miki kwarai da gaske!" Wata mai aikin sa-kai ta amsa cewa: "Dakata mini kadan, bari in duba maka!"
1 2 3 4 5
|