Sabuntawa Nan TakeDakika 10Dakika 30Sabuntawa Bisa Bin MatakaiSabuntawaKariSin na maraba da ’yan jaridar duniya da su halarci bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da na tafarkin murdiyaZa a gudanar da bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da Sinawa suka yi da yakin kin tafarkin murdiya da al’ummun duniya suka samu a nan birnin Beijing. Kuma Sin na maraba da zuwan ’yan jaridar kasa da kasa don su labarta wannan muhimmin lokaci. Dadin dadawa, Sin ta bude shafin yanar gizo mai adireshin http://kzjn80reg.zgjx.cn don saukaka yin rajista ga ’yan jaridar duniya da na yankunan Hongkong da Macao na Sin, kuma tana gayyatar ’yan jaridar da su yi rajista ta wannan hanya bisa gaggarumar maraba. Za a iya yin rajista ne daga raneku 15 zuwa 29 ga watan nan da muke ciki. Ban da wannan kuma, Sin za ta kafa cibiyar yada labarai yayin bikin ta yadda ’yan jarida na gida da na waje za su tafiyar da aikinsu cikin sawaba. Cibiyar za ta sauke nauyin dake wuyanta na maraba da ’yan jarida da gabatar da tarukan manema labarai daban-daban da ba da jagoranci ga aikin neman labarai da kuma kafa shafin yanar gizo na cibiyar da na WeChat, ta yadda za a yi amfani da fasahar intanet don baiwa ’yan jaridar hidimomi. (Amina Xu)Sauran LabaruSin ta amince da shiga rukunin masu sa hannu kan sanarwar New York05-Sep-2025Putin ya yaba da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba ga ‘yan Rasha05-Sep-2025Kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan Adam05-Sep-2025Sashen cinikayyar bayar da hidima na Sin ya bunkasa cikin watanni bakwai na farkon shekarar bana05-Sep-2025Ci gaban sojojin Sin yana hidimar manufar zaman lafiya a ko da yaushe05-Sep-202520250905-Yamai05-Sep-2025An shirya bikin tunawa da tarihi da martaba zaman lafiya a birnin Nanjing05-Sep-2025Kasar Sin ta kasance muhimmin karfi dake tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya05-Sep-2025Jami’an kasa da kasa sun yi matukar jinjinawa jawabin Xi Jinping05-Sep-2025Jakadan kasar Sin dake Najeriya ya gana da karamin ministan harkokin jin kai da rage talauci na kasar05-Sep-2025